fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Kalli abokin dan shugaban kasa da sukayi hadarin babur tare: Shima yana can asibiti kwance yana jiyya

Rahotanni suna kara bayyana dangane da hadarin da dan gidan shugaban kasa, Yusuf Buhari yayi akan mashin din tsere, wanda yayi sanadiyyar ji mishi ciwo akai sannan kuma ya karya kafa, Kafar watsa labarai ta Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Yusuf Buhari suna tseren mashin dinne shi da abokinshi, Bashir Gwandu, wanda ake iya ganin hotonshi a sama, lokacin da hadarin ya faru.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shaidun gani da ido da suka bayyanawa Daily Nigerian yanda bin ya faru sun bayyana cewa Yusuf da bokinnashi, Bashir suna tsere, Bashir din ya shiga gaban Yusuf, sai Yusuf ya fallo da gudu da nufin ya wuce Bashir din, anan ne, tsautsai, sai mashin din ya kwacewa Yusuf, ya bugi mashin din Bashir suka fadi.

Sun dan dauki lokaci a kwance a gurin, dan saida masu tsaron lafiyar Yusuf din suka tambayi izinin daukarsu zuwa Asibiti daga gurin danginshi sannan aka kwashesu zuwa Asibitin.
Shima Bashir yana can kwanci yana jiyya a asibitin da aka kwantarda Yusuf dan shugaban kasa, amma ba’ajin labarinshi, saboda labarin rashin lafiyar dan shugaban kasa, Yusuf ya shafe nashi.
Muna fatan Allah ya basu lafiya, yasa kaffarane.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  An buƙaci masallatai da coci-coci su rage hargowa cikin dare

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *