Sanata Farfesa Nora Dadu’ut ta sha da kyar a hannun matasa da suka sakata gaba a mazabarya kuma mahaifarta dake Namu a jihar Filato.
Lamarin ya farune a jiya, Alhamis, inda matasan suka kona motocin dake cikin tawagar sanatar ciki hadda na jami’an tsaro dana ‘yan jarida.
Saidai ita ta sha da kyar.
Sahara Reporters ta ce sanar taje garin nasu ne dan tuntuba akan yanda zata sake cin zabe a karo na 2.
Wata majiya tace matasan sun tsare wasu daga cikin wanda aka je taron dasu sun hanasu tafiya kuma sun sha karfin jami’an tsaron da aka kai wajan.
Tuni dai aka saka dokar hana fita a garin na Namu.
Southern Plateau Senator, Prof. Nora Dadu'ut was attacked in her hometown Namu this evening. The process was later on hijacked by thugs. Pls guys let's avoid Violence. Your #PVC should be ur Vawulence #GoRegister I'm from Southern Plateau and not happy with this act. pic.twitter.com/Lg325VY8l0
— Shepherd Yaddat Manfa (@SY_Manfa) April 28, 2022


