Ran gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya baci sosai bayan da ya bayar da Naira Miliyan 100 a kwashe kwata amma ba’a yi aikin da kyau ba.
A wani Bidiyo da ya bayyana a kafafen sada zumunta,an ga gwamnan na nuna bacin ransa bayan da ya ga yanda aka gudanar da aikin ba da kyau ba.
Nan take yasa aka kira dan kwangilar da yayi aikin dan ya zo ya duba.
Mutane da yawa sun bayyana ra’ayinsu kan lamarin da bayyana mamakin kashe Naira Miliyan 100 wajan kwashe kwata kawai.