fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai suka yi zanga-zangar kiyayya da takarar Tinubu saboda ya dauki musulmi a matsayin abokin takararsa

Wasu gamayyar Fulani da Hausawa daga Arewacin Najariya, musulmai sun yi zanga-zangar nuna kiyayya ga takarar dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu.

 

Sun bayyana hakane a zanga-zangar da suka yi a jiya yayin da Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

 

Shugaban wannan zanga-zangar, Abdullahi Bilal Mohamadu Ya bayyanawa manema labarai cewa, wannan rashin Adalci ne.

Yace abinda suke neman shine a baiwa kirista mukamin mataimakin shugaban kasar, kuma ba zasu daina wannan zanga-zangar ba har sai abinda hali yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.