Bayan kammala zaben fidda gwanin dan takarar PDP na shugaban kasa da Atiku Abubakar ya lashe, sauran ‘yan takarar sun taya Atiku murna amma banda Wike.
Wike shine ya zo na 2 bayan kammala zaben a bayan Atiku Abubakar.
Saidai an zargeshi da cewa bai taya Atiku Abubakar murnar zaben ba.
A wani bidiyo da aka ga ya bayyana a shafukan sada zumunta, Anga ynda Gwamna Wike ya duka yake gaishe da Atiku Abubakar.
The Exact Moment Wike Bowed To Atiku #PresidentAtikuGodWilling pic.twitter.com/0sQCQ7zogo
— Reno Omokri (@renoomokri) May 29, 2022
Wannan dai na nuna irin girman da Wike ke baiwa Atiku, hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omkri ne ya wallafa haka a shafinsa na sada zumunta.