Friday, February 14
Shadow

Kalli Bidiyo:An kama Jami’in Hizbah a Kano cikin masu tallata aikin Lùwàdì da Màdìgò

Rahotanni daga jihar Kano na cewa an kama wani da ke ikirarin shi jami’in Hisbah ne dake tallata ayyukan luwadi da Madigo a jihar.

Mutumin wanda yace sunansa, Idris Ahmad shine ke kula da bangaren kula da lafiya na Hisbah,kamar yanda yace.

An ganshi a wani Bidiyo yana bayyana cewa, ‘yan Luwadi da Madigo suma mutanene kamar kowa kuma ya kamata a canja dokar data ce a rika hukuntasu har tsawon shekaru 14 da Gwamnatin tarayya ta saka.

A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne dai aka yi wannan doka inda yace ba zai amince da yarjejeniyar halatta Luwadi da Madigo ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yara 'yan shekaru 15 zuwa 16 su 3 uwarsu daya ubansu daya wanda aka dauka daga Najeriya aka kaisu suna ka-ru-wan-ci a kasar Ghana

Saidai bayan yekuwa akan waccan magana da Idris Ahmad yayi, an kamashi.

Bayan da aka kamashi, ya bayyanawa manema labarai cewa tabbas shine a wancan bidiyo amma bai san ma me ake nufi da LGBTQ ba a lokacin da yayi wancan jawabi.

Yace kuma yayi jawabinne a Sabon Gari dake Kano.

Saidai da aka tambayeshi me yasa bai yi bincike kamin yin waccan magana ba, bai amsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *