Fim din Makaranta ya jawo cece-kuce sosai tun kamin fitowarsa kasuwa bayan ganin tallarsa a shafukan sada zumunta.
Hukumar tace fina-finan Kano na neman wanda ya shirya fim din ruwa a jallo amma yace shi ba dan ‘yan Kano yayi fim dinsa ba dan haka babu wanda ya isa ya kamashi.
Aminu Umar Mukhtar ya bayyana a hirar da BBC ta yi dashi cewa, ba dan Hausawa ko ‘yan Kano yayi fim din ba, kuma yayi yaruka daban daban a cikinsa.