Wani faifan bidiyo na wani jami’in kwastam na Najeriya yana mari wani hadimin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya bayyana a yanar gizo.
Dan rajin kare hakkin dan Adam, Harrison Gwamnishu, ya raba bidiyon a daidai lokacin da jami’in kwastam ya mari Mista Samson Nwachukwu a kan babbar hanyar Benin/Agbor a ranar Asabar, 7 ga Afrilu, a gaban abokin aikinsa da wani jami’in soja.
A cikin faifan bidiyon, ana iya jin dan sandan a fusace yana tambayar wanene Mista Samson Nwachukwu bayan ya shaida masa cewa shi mataimaki na musamman ne ga gwamnan jihar Delta kafin ya yi masa mari. Bidiyon ya ƙare tare da jami’in soja yana gaya wa jami’in kwastam ya “sake wannan mutumin.”
Ko da yake, Gwamnishu bai bayyana abin da ya kai ga faruwar lamarin ba, amma ya sha alwashin nema wa Mista Nwachukwu hakkinsa.
Kalli bidiyon a kasa..
https://www.instagram.com/p/CdS9sRHtbMt/?igshid=YmMyMTA2M2Y=