fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Kalli bidiyon yadda wani kwarto ya diro daga gidan sama a lokacin da mijin budurwarsa ya dawo gida

Wani kwarto ya tsallake rijiya da baya daga hannun mijin wata mata da ya ke lalata da ita a gidan aurenta.

Matar auren ta gayyace shi gidan su da ke Lekki a jihar Legas lokacin da mijinta ya fita ya dawo ba tare da ta sani ba, sai ta tilasta wa saurayin tserewa ta hanyar bayan gida.

Wani makwabciyarsu ta kama shi a lokacin da yake kokarin dirowa daga benen gidan.

Ana iya ganinsa yana tsalle-tsalle daga ginin ya sauka a kasa inda ya dauki tufafinsa ya fara gudu.

Makwabciyar ta ce uwar gida ta kan kawo maza gida a duk lokacin da mijinta ba ya nan.

Kalli bidiyon a kasa….

https://www.instagram.com/reel/CesxtFeOad-/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.