Wadannan wasu masu garkuwa da mutanene da aka kama a jihar Ekiti.
Wadanda aka kama din sune Abashe Adamu Idris, da Ibrahim Mumini Toyin.
Kakakin yansandan jihar, DSP Sunday Abutu ya bayyana cewa wanda aka kama din sune ake zargin na da hannu a garkuwa da mutane da yawa a jihar.
Yace bayan lokaci me tsawo sun yi nasarar kama wanda ake zargin kuma idan suka kammala bincike zasu gurfanar dasu a gaban kuliya.