Bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda aka ce na gwamnatin jihar Zamfara ne dake Abuja.
An ga cewa an kwashe komai na gidan.
An dai zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle da mukarrabansa da yin wannan aika-aika.
Dama dai Gwamna Lawal Dare ya zargi cewa tsohon gwamnan ya tafi da motoci na Bikiyoyin Naira mallakin gwamnatin jihar inda yace ya bashi lokaci ya dawo dadu.