Wani magidanci ya ziyarci Asibiti, rai hannun Allah bayanda matarsa ta lakada masa duka.
Mutumin me suna Niyi Adeyemo dan kimanin shekaru 39 na zaunene a yankin Ikosi-Ketu dakw birnin Legas.
Kuma Rahotanni sun bayyana cewa yana fama da ciwon gabobin jiki.
Magidancin yace matsalarsu ta fara tashine tsakninsa da matarsa bayan da mahaifiyarsa ta je gidansu amma matar tasa ta nuna bata son ‘yan uwansa na zama a gidan nasu.
Ya kara da cewa, matar tasa ta je ta sameshi bayan dawowa dsga Dubai inda take neman ya saketa amma yaki, yace nan fa ta yaga masa kaya ta fara dukansa.
Yace har saida ya suma daga baya ya ga kansa a Asibiti.
Saidai ita matar ta yi ikirarin cewa, ta ji ciwo a fadan da ya faru tsakaninta da mijinta inda itama ta kai kara wajan ‘yansanda.