Wani matashi dan kasar Ghana mai shekaru 25, Muima ya bayyana cewa yanaso ya auri wata mata yar shekara 85 mai suna Thereza.
Inda ya bayyana cewa sun fara haduwa matar ne bayan da suka nemi hayan gidanta tare da abokansa, wanda daga nan ne ta fara kiranshi da mijina.
Kuma ya kara da cewa itace ra’ayin shi kuma ita yake so kamar kowa yake da wacce yake so ya aura.