‘Yar Najeriya dake da dangantaka da kasar Italiya, Victoria Oluboyo ta zamo bakar fata ‘uar Afrika ta farko data samu kujerar mulki a kasar Italiya.
Victoria tayi nasarar lashe zaben kansilan gatin Parma ne dake kasar ta Italiya.
Wani dan Najeriya dake zama a kasashen waje Olufemi Iyanda ne ya wallafa wannan labarin a shafinsa na Facebook.
Inda yace kasar Najeriya ta fara samun daukaka a kasashen turai musamman a kasar Italiya inda ake daukar su a matsayin karuwar da kuma masu safarar kwaya.