fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Kalli hoto:’Yanda ‘yan daba suka shiga cikin masallaci suka kona wani malami saboda yana wa’azi

Lamarin ya faru makonni 2 da suka gabata, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

 

Malam Aliyu Muhammadu Tukur yana wa’azi cikin masallaci yayin da ‘yan dabar suka shiga har cikin masallacin suka banka masa wuta.

 

Sun yi hakan ne saboda yana magana akan zaben shekarar 2023, Malamin yana garin Kumo ne na karamar hukumar Akko dake jihar Gombe.

 

Yace ya godewa Allah da basu kasheshi ba dan abinda ya kaisu kenan amma sun jikkatashi sosai.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Mahid Muazu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wadanda ake zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.