Ƙungiyar IS ta wallafa wani bidiyo da take ikirarin kashe fararen hula 20 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta masu tayar da ƙayar bayar da ke ayyukanta a yankin da sunan ISWAP ta ce mutanen da ta nuna ta kashe a bidiyon “kiristoci” ne.
Har yanzu hukumomi ba su ce komai ba akan bidiyon.
Biidyon wanda ƙungiyar ta wallafa a intanet ya nuna kaso uku na mutane daban-daban a kayan fararen huka – da ke nuna mutum huɗu da 11 da kuma mutum biyar a kowace tawaga, kuma dukkansu maza ne.
Sannan ga alama a wurare daban-daban mutanen suke – waɗanda ƙungiyar ta ce duka a jihar Borno ne.
Babu tabbas kan lokacin da aka ɗauki bidiyon.
Bidiyon ya nuna ƴan ƙungiyar da fuskarsu a rufe ɗauke da bindigogi kuma mai magana da yawunsu yana wulwula wuƙar da ke hannunsa.

In a major boost, troops of the 402 Special Forces Brigade, comprising of 134, 198 and 199 Special Forces Battallions, under the Operation Hadin Kai's second phase of Desert Sanity, cleared the terrorists camps in the axis of Bama Local Government Areas. pic.twitter.com/OBZGbW0T6b
— Zagazola (@ZagazolaMakama2) May 4, 2022
Da yake magana da Hausa, mutumin ya ce sun kashe mutanen ne don ramuwa ga kashe shugabanninsu biyu da aka yi a yankin Gabas Ta Tsakiya a farkon shekarar nan.
BBC ba ta iya tabbatar da ikirarin mutanen ba a karan kanta na cewa mutanen kiristoci ba ne, ko kuma inda ainihin abin da ya farun.