Saturday, July 13
Shadow

Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima

Wani abin mamaki da ya dauki hankulan ‘yan Najeriya shine ganin yanda gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim ya fi na mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris kyau.

Gidan na Mataimakin shugaban kasar Najeriya an ginashi ne akan Naira Biliyan 21 duk da cewa akwai wani gidan mataimakin shugaban kasar, a yanzu mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima gidaje biyu gareshi.

A yayin da ita kuma mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris gida daya gareta.

Gidan mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris.

Bayan kashe Naira Biliyan 21 wajan gina sabon gidan na mataimakin shugaban kasar Najeriya da gwamnatin Tinubu ta yi ta kuma kashe Naira Biliyan 2.5 wajan gyara tsohon gidan mataimakin shugaban kasar duk da yake cewa ko da ba’a gyarashi ba, zai iya zama a cikinsa lafiya lau.

Karanta Wannan  Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

A lokacin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya hau Mulki, Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo yace ba ruwansa da gidan mataimakin shugaban kasar saboda wanda yake ciki ya isheshi saboda gwamnatinsu ta yiwa al’umma aiki ce.

Saidai daga baya gwamnatin Buhari ta ware kudin gyaran wannan gida inda aka ware Naira Miliyan 250 akan gina gidan me gadin gidan kawai.

Saidai Shugaba Buhari bai samu damar kammala wannan gida ba inda sai shugaba Bola Ahmad Tinubu ne ya kammalashi.

A yayin da a Najeriya, gwamnati ce ke kashe kudi dan gyara gidan mataimakin shugaban kasa, a kasar Amurka, Mataimakin shugaban kasar ne da kansa yake gyara gidan idan yana so daga aljihunsa ba daga asusun baitul mali na gwamnati ba.

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata takwas

Ko kuma a bada taimako daga ‘yan kasa su gyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *