fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Kalli hotuna gwanin ban tausai yanda wani tsoho ya cire rufin gidansa ya sayar dan ya biya kudin fansa a sako dansa da ‘yan Bindiga suka kama a Katsina

Wani tsoho ya dauki hankula sosai inda mutane suka ta bayyana alhini kan lamarin.

 

Ya cire rufin gidansa ya sayar dan a hada kudin da za’a karbo dansa daga hannun ‘yan Bindiga.

 

Mutumin me suna Sa’idu Faskari ‘yan Bindigar sun saceshi, amma da dansa ya je biyan kudin fansa na Naira dubu 50, sai suka kama dan nashi shi kuma suka sakeshi.

 

Premium times ta ruwaito cewa, ‘yan Bindigar a yanzu suna neman a biyasu 100,000 dan su saki dan nasa.

Karanta wannan  So makaho ne: Wata matashiya 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin sahibinta mai dauke da cutar kanjamau

 

Shi kuma yace na abinci ma yake fama dashi ballantana ya samo wadancan kudin, shiyasa yake son sayar da rufin gidansa.

 

Hukumar ‘yansandan jihar bata ce komai ba akai tukuna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.