fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Kalli Hotuna: Yanda Bam ya kashe mutane da dama a wata makaranta

Mutum kusan 60 ake fargabar sun mutu bayan wani bam ya tashi a wata makaranta a gabashin Ukraine, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da sojojin Rasha da ƴan aware.

Gwamnan yankin Luhansk, Serhiy Gaidai, ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yana mai cewa mutum 60 ne ake fargabar sun mutu a ƙarƙashin ɓaraguzan makarantar da ke Bilohorivka.

Ya kara da cewa, kimanin mutane 90 ne ke zaune a cikin ginin kuma an ceto 30, bakwai daga cikinsu sun samu raunuka.

Mista Gaidai ya ce wani jirgin Rasha ne ya jefa bam a ranar Asabar.

Karanta wannan  Kalli hotuna yanda soja dan arewa ya ajiye aikin soja dan yiwa Peter Obi yakin neman zaben shugaban kasa

Ba a iya tantance zargin nasa kai tsaye ba kuma babu wani martani da Rasha ta mayar.

Luhansk ya kasance yanki na fagen yaƙi yayin da sojojin Rasha ƴan aware ke neman yi wa dakarun gwamnatin Ukraine ƙawanya dakarun gwamnati, tsawon watanni biyu da fara mamayar Rasha.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.