Fada ya barke tsakanin Inyamurai da yarbawa a jihar Akawa-Ibom inda har mutane 5 sun mutu, an kuma tafka asarar miliyoyin Naira.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Ibeno ta jihar.
Fadan ya fara ne tsakanin wata kungiyar matsafa, kamin da ga baya ya rikice ya koma na kabilanci.
Tuni dai Yarbawan suka fara tserewa yayin da inyamuran suka rika wawason kayansu da kona wasu.

