Akwai ‘yan majalisar tarayya da suka shafe shekaru 20 suna sanatoci a majalisar wanda ta kai ga ana kiran cewa majalisar ta zama tasu.
Ga dai sunayensu kamar haka;
Na farko dai akawai Nicholas Mutu daga jihar Delta.
Akwai kuma Ahmad Lawal wanda shima tun shekarar 1999 yake majalisar, yana wakiltar jihar Yobe.
Akwai Sanata Ali Ndume daga jihar Borno wanda shima tin shekarar 1999 yake majalisar.
Akwai Ike Ekweremadu daga jihar Enugu wanda shima tun shekarar 1999 yake majalisar.
Akwai kuma James Manager daga jihar Delta wanda shima yana majalisar tun shekarar 1999.
Akwai kuma Leo Ogor daga jihar Delta.
Sai kuma Femi Gbajabiamila na majalisar Wakilai.