Gadar sama kenan da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yake ginawa da kudin haraji da gwamnatinshi ta tara dake kan titin Katsina cikin binin Kano, wannan hoton na sama yanda ake so gadar ta kasancene bayan kammala ginata.
Hotunan nan na kasa kuwa yanda ake ginin gadar ne a yanzu haka.
Ana saran a cikin wannan watan da mukene idan Allah ya yarda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar ta Kano inda zai bude katafariyar gadar kasa ta hanyar Fanshekara da aka kammala kuma zai duba yanda ake aikin wannan gada da titin Katsina