fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Kalli kayataccen, babban masallacin kasar Jamus da aka ginashi kan kudi sama da naira biliyan takwas

Wannan shine masallacin birnin Cologne na kasar Jamus, birni na hudu mafi yawan mutane a kasar, Kafin gina masallacin an samu tirjiya daga wasu mazauna garin da suka rika ganin cewa wannan ginin masallacin zai iya haddasa karuwar yawan musulmai a garin. Dayake wata hukumar kula da addinin musulunci ta kasar Turkiyya na cikin wadanda suka bayar da gudummuwar kudin gina masallacin, ‘yan Birnin Cologne din sun rika ganin cea ginin masallacin wata dabarace ta kara yawan musulmi da yada addini musulunci a kasar.

Wasu masu kishin garin na Cologne sunyi ta zanga-zanga akan baza’a gina masallacin ba, da suka ga hakarsu ba zata cimma ruwa ba, sai suka koma neman a rage girman masallacin, amma daga karshe an zauna akayi tattaunawa tsakanin masu fada aji na garin, aka kuma abayar da izinin ginashi.

Masallacin dai yana daya daga cikin manyan masallatai na nahiyar turai sannan kuma shine masallaci mafi girma a kasar ta Jamus.

An ginashi akan kiyasin kudi Yuro miliyan sha bakwai zuwa miliyan ashirin, kwatankwacin sama da naira biliyan takwas. Wadanda suka bayar da tallafin kudin ginin masallacin sun hada da Wata kungiyar ko kuma hukumar kula da addinin musulunci me suna DITIB a takaice, wadda take karkashin kukawar kasar Turkiyya, sai bashin banki, tallafi daga wasu kungiyoyin addinin musulunci guda dari takwas da tamanin da hudu, da kuma wata cocin garin ta Cologne itama ta bayar da gudummawa.

Masallacin babbane sosai, an kiyasta zai dauki masallata dubu biyu zuwa dubu hudu, kuma a cikin ginin masallacin akwai gurin sayar da abinci da dakunan taro da shagunan sayar da kaya, wadanda har wanda ba musulmi ba zasu iya yin amfani dasu.

An dai kammala ginin wannan masallacin a cikin wannan shekarar ta 2017 da muke ciki.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *