fbpx
Monday, June 27
Shadow

Kalli kayataccen bideyon Mohammed Salah tare da kadan daga cikin tarinsa yayin da ya cika shekara 30

Tauraron dan wasan Liverpool, Mohammed Salah ya cika skekaru 30 a yau ranar laraba 15 ga watan Yuni.

Mohammed ya kasance daya daga cikin zakarun ‘yan wasan Firimiya na tarihi bayan dayi nasarar ciwa Liverpool kwallaye 156 a wasanni 254 daya buga mata.

Kuma ya kasance dan wasan Afrika dayafi cin kwallaye masu yawa a gasar inda yaci 120, sannan shine dan wasan fi ciwa Liverpool kwallaye masu yawa a gasar zakarun nahiyar turai, inda yaci mata guda 33.

Salah yayi nasarar lashe kofuna masu yawa a kungiyar wanda suka hada da kofin gasar zakarun nahiyar turai, Firimiya, Super Cup, Lig Cup da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.