fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Kalli Kuskuren Bezema da ya jawowa Real Marid rashin nasara a hannun Real Betis

Wasa ya jikewa Real Madrid jiya, Lahadi bayan Real Betis ta lalasa ta da ci 2-1 a wasan da suka buga na gasar cin kofin La liga.

 

Wannan sakamako yasa Madrid ta rikito daga saman Teburin na gasar inda ta koma ta 2 yayin da babbar abokiyar takararta, Barcelona ta dare saman teburin gasar da tazarar maki 2.

 

Dan wasan Real Madrid, Casemiro jikinshi yayi sanyi sosai inda yace wannan rashin nasara da suka yi watakila shikenan ba zasu dauki kofin La liga ba.

 

Yanzu dai Real Madrid na da sauran wasanni 6 da zata buga a gidanta, Santiago Bernabeu sai kuma wasanni 5 da zata buga a waje. Ita kuwa Barcelona na da sauran wasanni 5 a gida, shida a waje.

 

Zidane ya sha suka daga wajan magoya bayan kungiyar, musamman a shafukan sada zumunta inda aka rika caccakar salon wasan da ya buga.

 

Saidai wani abu da ya fi daukar hankali shine kuskuren da Kareem Benzema yayi da ya jawowa Real Madrid aka ci ta kwallo ta 2.

 

Benzema ya bar gaba inda yake bugawa ya koma baya neman kwallo. Ya samu kwallon saidai garin baiwa Ramos da ke can nesa dashi, sai bai buga kwallon da kyau ba, ta kuma samu dan kwallon Real Betis, Cristian Tello wanda kuma tsohon dan wasan Barcelonane.

 

Shi kuwa be yi wata-wata ba da wannan dama inda ya je ya likawa Marid kwallo ta 2 wanda a haka aka tashi wasan.

 

Saidai duk da haka, kocin Real Madrid, Zinedine zidane ya dauki alhakin rashin nasarar inda yace Lefinsa ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *