Matashin Najeriya dan gani kashe nin ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa muddin Amaechi be fito takarar shugaban kasa ba to zai kashe kansa.
Yace yana ta karanta bakin labarin cewa, Amaechi be son zama shugaban Najeriya, yace yana fatan wannan labari na karyane.
Yace dan ba zai fahimci ace masa ministan da ya fi kowane iya aiki ba wanda zai iya kawo karshen matsalar tsaro, da kuma Adalci ace wai ba zai so zama shugaban Najeriya ba.
Yace idan da gaskene cewa amaechi be son tsayawa takarar shugaban kasa gaskiya bai musu Adalci ba kuma idan yayi hakan to shi zai kashe kansa.

