Wani me tsaron makabarta, Kushimo Lukman dake jihar Ogun ya shiga hannun jami’an tsaron bayan da aka kamashi ya hako gawar wani karamin yaro ya yanke kan gawar.
An kamashi bayan da aka sha dambe dashi amma aka fi karfinsa.
Bayan kamashi, ya amsa laifinsa inda yace wanine ya sashi kuma zai bashi ladar Dubu 50.
An dai fara farautar wanda ya sashi wannan danyen aiki, inda shi kuma aka kaishi ofishin ‘yansanda.