Wannan wata motar tafi da gidankace, wadda kusan komi da ake bukata na gudanar da rayuwar yau da kullun akwaishi a cikinta, idan ma mutum ya kirata da sunan gida, bata baci ba, domin banbancinta da gida, shine ita tana tafiya daga wani guri zuwa wani guri, shi kuwa gida a guri daya kawai yake.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kamar yanda muke gani a hoton sama, akwai garejin ajiyar mota, wadda girmanta be wuce kimaba.
Ita dai wannan mota, kamar yanda rahotanni suka bayyana ana sayar da itane akan kudi dalar amurka miliyan daya da dubu dari bakwai.
Wannan gurin zamane na shakatawa dake cikin motar.
Wannan kuma dakin kwanane da gurin wanke hannu/baki dadai sauransu dake cikin motar
Nan gurin zaman direbane, da kuma irin na’urorin dake gaban motar da zai iya yin amfani dasu.
Nan gurin dafa abincine na cikin motar.
Nan kuma gurin ajiye kwanuka dakofi ne na cikin motar,
Cikakken hoton dakin kwana na cikin motar.