Fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau kenan a gurin wani taron daren Arewa a kasar Cyprus inda daliban jami’ar Estern Mediterranean ‘yan Arewa dake kasar suka shirya a daren jiya.
Taron dai an shiyashine inda aka nuna al’adu irin na Arewacin Najeriya da ma sauran kabilun kasarnan, anga Rahama Sadau a guein taron saye da atamfa, dama dai mujallar Fim Magazine, a cikin kwafin data fitar na wannan watan ta bayyana cewa Rahamar ta tafi kasar ta Cyprus inda zatayi watanni uku acan.