fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Kalli Sabon saurayin Hadiza Gabon da suka hadu ta yanar gizo

 Wani bawan Allah me suna Muhammad Bilal Omas daya dade yana bayyana irin yanda yake matukar kaunar tauraruwar fina-finan Hausa, Haida Gabon burinshi ya cika jiya, dan kuwa ita Hadizarce da kanta ta kirashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Muhammad dai ya jima yana ta kwarmata soyayyarshi ga Hadiza Gabon a dandalinshi na sada zumunta da muhawara kuma ya bayyana cewa ba da wasa yake ba, a haka ya samu wani wanda yake tunanin yana kusa da Hadizar ya rokeshi ya bashi lambar wayarta amma be bashiba.

Da yaga dai da gaske bazai bashiba, sai kawai ya sake komawa dandalinshi na sada zumunta ya wallafa cewa to tunda  yaki bashi lambar Hadizar shi ga lambarshi ta taimaka ta kirashi

Ai kuwa sai yayi sa’a Hadizar ta dauki lambarshi ta kira, batan da aka jawo hankalinta akai.
Muhammad dai ya bayyana jiya Laraba a matsayin ranar da bazai taba mantawa da ita a rayuwarshi ba, kuma yayi fatan Allah ya sakawa wannan soyayya tasu Albarka.
Muma muna musu fatan Alheri, Allah yasa su fahimci har takai ga aure.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Mun nunawa Abba Gida-Gida Soyayya amma ya nuna mana kiyayya>>Inji Wani da aka rushewa shago a Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *