
Wasu lokutan akan danganta daukar kayan da suka wuce kima akan abin hawa da Najeriya kokuma kasashen Nahiyar Afrika. Duk da cewa ba abin arzikibane, amma wadannan hotunan sun nuna cewa ba kasashen Afrikane kawai ake samun mutane da daukar kayan da suka wuce kima akan abin hawaba. Misali, wannan mutumin da ake ganin hotonshi a sama, dan kasar indiyane ya dauko kwallayen roba da suka wuce kima akan kekenshi.

Wanan kuma wasu ‘yan kasar Bangladesh ne suka dauko durom-durom da ba komai a cikinsu da suka wuce kima a akan wani amalanken.

Wannan hoton ginin wata cocice da aka daukota akan wata mota ta musamman, ana canja mata gurine daga wani gari zuwa wani gari, bayan da masu ibada a ciki suka canja gari, wannan ya faru a kasar jamus, shekarar 2007.

Wannan wasu falasdinawane da amalankensu ya tintsire saboda kayan da suka dorawa jakin dake jansu ya mishi yawa.

Wasu mutane dauke da damman kaya akan amalanke, a kasar China.

Wannan kuma wata me ina da robobice a babban birnin kasar China, itama da baronta dake jibge da kayan da suka wuce kima.

Shekaran jiyane, mukaji labarin gwamnan jihar Nasarawa, umar Tanko Almakura ya hadu da wani me acaba, dauke da yara ‘yan makaranta, su biyar akan matsin daya, to ga waninan, dan kasar India, su shida, harshi, bakwai kenan, lokacin daya daukosu daga makaranta zai kaisu gida.
Wannan ma wasu ‘yan kasar Indianne, su shida akan mashin daya.

Wannan shima dai wani dan kasar ta Indiyane dauke da kwallayen roba fiye da kima akan keke Napep/A daidaita Sahu?Agwagwa da buje da nufin kaiwa kasuwa.

A kasar Indiya dai akaga wannan lodin mutane cikin mota daya wuce kima.

Wannan kuma wani dan kasar Kenyane dauke da kujerar zama akan mashin.

Wannan wasu ‘yan kasar fakistanne da motarsu, saboda tsabar lodin daya mata yawa, suna amfani da igiya dan su jata zuwa kasa.
Reuter/metro.uk