Wannan hotunan wata gawace da aka mata makara me siffar gida hadda tauraron dan Adam, wadannan hotunan sun dauki hankulan mutane sosai musamman a dandalin sada zumunta da muhawara na yanar zigo, lallai Imani ma wani abune, Allah mun godema, ka kara shiryar damu akan hanya madaidaiciya.
To amma dai wannan tabewar basira da yawa take kudin da suka kashe sukayi wannan makara, da abinci suka siya sai yafi musu amfani.
A cikin wadanda sukayi sharhi akan wannan hotunan wani yace, yana daya daga cikin abinda addinin musulunci ke birgeshi, irin yanda ake yin jana’izar mamaci cikin mutunci da sanin ya kamata.