Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki kenan yake gaishe da tsohon shugaban kasa Olisegun Obasanjo a lokacin da yazo gurin bikin diyarshi, satin daya gabata wanda akayi a garin Legas, irin yanda Sarajin ya gaishe da Obasanjo ya dauki hankulan mutane.
Wasu na ganin cewa yayi ne dan neman wani abu wasu kuma na ganin yin hakan ba komai bane a al’adar Yarbawa akwai girmama na gaba sosai.