Wannan dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabuwe ne Emmerson Mnangagwa wanda shine za’a rantsar a matsayin wanda zai maye shugaba Robert Mugabe da yayi murabus, Micheal Sean sunan dan nashi kuma a cikin wadannan hotunan an ganshi yana fariya da kudi, wanda hakan yasa wasu ke tambayar anya kuwa?.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ana tunanin an kori Robert Mugabe wanda yake tattare da zarge-zarge da suka hada dana cin hanci da rashawa, wanda shima a zamaninshi an zargi ‘ya’yanshi da matarshi da yin facaka da dukiyar kasar, to ga dan Emmerson shima kamar da alama babu canji.
Lallai ‘ya’yan manya suna jin dadinsu.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});