Awanni kadan da haihuwar wani jariri da ‘yan uwan juna mace da namiji suka haifa ya mutu bayan da aka haifeshi da wata kalar siffa da ba’a gani ba.
An haifeshine a Dustlik, dake Uzbekistan kuma likitoci sunce saboda ‘yan uwan junane suka haifeshi shiyasa yazo da irin wannan siffa.
Likitocin sunce sun yi iya bakin kokarinsu wajan kubutar da rayuwar jaririn amma abin ya faskara.
Sun kara da cewa matasa idan za’a yi aure a rika kiyayewa kada a auri dangi na kusa kuma a rika yin gwaji.
Sunce auren dagin juna na sa a haifi yaran da basu da lafiya.