Gwamnan jihar jihar Adamawa, Jibirilla Bindow kenan, jiya a garin Dong inda sukaje tare da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo dan ganin irin yanda rikicin kabilanci ya gudana a yankin, anyi kiyasin cewa, akalla mutane arba’inne suka rasa rayukansu dalilin wannan rikici.
Kuma a wannan hoton gwamnanne, dole tasa ya rufe hancinshi saboda warin gawarwaki dake zube a gurin.