An ga wani hoto dake nuna sojojin kasar Yahudawan Israela suna taka tutar kasar Saudiyya me dauke da kalmar shahada.
Lamarin ya jawo tayar da jijiyoyin wuya matuka inda da dama suka ce dama addinin musulunci ne kasar Israelan take yaka ba kasar Palasdinawa ba kadai.
Wasu dai na zargin kasar Saudiyya da kin daukar matakan da suka dace dan baiwa palasdinawa kariya daga kisan da kasar Israela take musu.