‘Yan dabar siyasa sun kaiwa ‘yan majalisar jihar Bauchi hari a ranar Litinin.
Lamarin ya sa mutane 6 sun jikkata, an lalata motoci da dama.
‘Yan dabar su kusan 50 ne suka kai harin, saidai tuni jami’an ‘yansanda sun kewaye majalisar.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka jikkata sun ce ‘yan dabar na dauke da makamai da suka hada hadda bindiga.