Monday, October 14
Shadow

Kalolin ruwan gaban mace

Kin taba tunanin ko kalolin ruwan dake fita daga gaban mace guda nawane? A wannan rubutun,mun kawo muku cikakken bayani kan yawan kalolin ruwan dake fita daga gaban mace da kuma ma’anar kowanne.

Ga su kamar haka:

Ruwan dake fita a gaban mace abune da yawancin mata sun saba dashi, kuma yana fitane dan wanke da tsaftace gaban macen daga lokaci zuwa lokaci.

Ba abune na tashin hankali ba amma ya kamata a lura da canje-canje a kalolin ruwan da kuma yanayin jiki wanda ka iya sanyawa a gane shigar cuta.

Fitar Farin Ruwa:

Farin ruwa wanda wani lokacin yakan iya zama me yauki ko me ruwa-ruwa a gaban mace bashi da matsala.

Wani lokacin ma zaki ga ya bata miki wando, a wani lokacin ida kina jin sha’awa zaki iya jin wannan ruwa wanda yana zuwane dan saukaka yin jima’i.

Hakanan kuma wannan farin ruwa alamace dake nuna cewa, idan aka yi jima’i dake, zaki iya daukar ciki.

Saidai idan wannan farin ruwa ya cika kauri da yawa sannan kuma ya rika fita da gudaji-gudaji to wannan alamace ta cutar Infection ko ace sanyi, wanda za’a iya sayen maganin Likita ko a hada a gida a shafa ko a sha.

Karanta Wannan  Alamomin budewar gaban mace

Ruwa me kalar Grey/Gray ko kalar Toka ba me duhu ba:

Idan kika ga ruwan dake fitowa a gabanki kalar Gray/Grey ne ko kalar toka ba me duhu ba to wannan ma alamar ciwo ne da ya kamata ayi maganinsa.

Wani lokacin wannan matsala ka iya jawo jin wari ko kuma jin zafi a lokacin da ake fitsari.

Kina iya sayen maganin antibiotics a kemis ki sha, yana maganin wannan matsala sosai.

Idan ba’a warke ba bayan kwanaki biyu sai a tuntubi likita.

Fitar Jan Ruwa:

Fitar Jan Ruwa a gaban mace ba matsala bane, yawanci yana da alaka ne da jinin al’adarki, dan haka ba alamace dake nuna rashin lafiya ba.

Mata kala-kala ne, wata jininta na zuwa da kauri yayin da wata kuma nata ke zuwa babu kauri.

Hakanan za’a iya ganin fitar Jan ruwa a gaban mace idan ta daina shan maganin tazarar haihuwa.

Akwai kuma jini wanda bana al’ada ba da mace zata iya gani.

Saidai idan ya tsananta, yana iya zama matsala, Wanda ya kamata a tuntubi likita.

Hakanan wannan fitar jan ruwa a gaban mace na iya zama alamar zubewar ciki watau bari, idan kina da danyen ciki kika ga jan ruwa na fita a gabanki, ki tuntubi likita dan jin karin bayani.

Karanta Wannan  Fitar farin ruwa mai kauri

Fitar Ruwa me kalar kasa/Brown:

Idan jini ya dade, yakan canja kala daga jaa ya koma ruwan kasa. Wannan ne zai iya sawa ki ga ruwa me kalar ruwan kasa na fita daga gabanki.

Ganin irin wannan ruwa ba matsala bane, yakan iya zama jinin al’adane da yayi jinkiri ko kuma sanadiyyar yin tazarar haihuwa.

Idan kina da tsohon ciki, zaki iya fuskantar wannan matsala ta fitar jini a gabanki me duhu, wannan ba matsala bane, zai iya fita a lokaci guda, zai iya kuma rika fita a hankali, Wannan alamace dake nuna jikinki ya fara shirya haihuwar abinda kike dauke dashi.

Fitar ruwa kalar Pink ko kuma kalar tsatsa:

Fitar ruwa me kalar tsatsa ko kuma ace pink ba matsala bane a mafi yawan lokaci, irin wannan ruwa yakan fita a farkon fara jinin al’ada.

Hakanan irin wannan ruwa yakan fita bayan an gama jima’i ga wasu matan.

Hakanan matan da suke shirin daukar ciki ko kuma ciki ya riga ya shiga a kwanakin farko ana iya ganin irin wannan ruwa.

Karanta Wannan  Yaya kalar ruwan ni'ima yake

Fitar ruwa me kalar Green, kore ko ace kalar ganye:

Fitar ruwa me kalar ganye ko kore daga gaban mace alamace dake nuna an kamu da cutar Infection ko ace sanyi. Hakanan ruwan zai iya zama me yawa ko kuma ya zamana yana da wari.

Hakanan akwai sauran wasu cutuka da ake dauka yayin jima’i dake sanya fitar da ruwa kalar kore a gaban mace.

Cutar yoyon fitsari ma na sa fitar da ruwa kalar kore a gaban mace.

Yana da kyau idan aka ga irin wannan a tuntubi likita.

Fitar ruwa kalar Yellow ko ruwan dorawa:

Yawanci fitar ruwa kalar Yellow ko ace kalar dorawa a gaban mace ba matsala bane, yakan iya zama sanadiyyar haduwar farin ruwan da ya saba fita a gabanki da jini.

Ana kuma iya ganin wannan ruwa kamin zuwan jinin al’ada ko kuma idan jinin al’ada ya dauke da wuri.

Saidai a wasu lokutan wannan ruwa ka iya zama alamar wata cuta ko kuma reaction na wani abu da kika ci musamman idan akwai kore a cikinsa, yana kuma iya zama alamar wata cutar da aka dauka wajan jima’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *