fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kamar beraye muka boye lokacin da ‘yan ta’adda suka kawo hari kurkukun Kuje, Abba Kyari ya roki kotu ta bayar da belinsa

Babban dan sandan da aka dakatar wato DCP Abba Kyari ya roki babbatar kotun tarayya cewa ta bayar da belinsa saboda matsalar tsaro ta gidan Kurkukun Kuje.

Inda ya bayyana cewa kamar beraye haka suka boye a lokacin da ‘yan ta’addan ISWAP suka kawo hari gidan kurkukun da ake tsaronsa.

Amma NDLEA ta sake gabatarwa da kotun shaoda ta uku yau wadda ke tabbatar da cewa DCP Abba Kyari ya basu cin hancin dala 61,400 don kar su kama shi akan safarar miyagun kwayoyin dayake yi.

Karanta wannan  Naira miliyan 650 masu garkuwa da mutane suka samu a cikin shekara guda-Bincike

A karshe dai alkali Emeka Nwite ya dage sauraron shari’ar belin nasa izuwa 30 ga watan Augusta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.