Kungiyar kare muradin Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa matsalar Tsaron Najeriya ta isa ace shugaba Buhari ya canja manyan jami’an tsaron da kuma canja salon yaki.
Kungiyar ta yi magana da bakin kakakinta, Yinka Odumakin inda tace bai kamata ace tunda dai shugaban kasar bai gamsu da aikin da shuwagabannin tsaron suka yi na shekaru 5 ba ya barsu su ci gaba da zama ba.
Yace gargadi kadai da shugaban ya wa shuwagabannin tsaron bai isa ba. Yace in ba haka ba Najeriya na cikin hadarin nutsewa.
Yace duka wasu kwanakine rikicin jam’iyyar APC ya dauka amma shugaban ya rusa kwmaitin gudanarwar Jam’iyyar to haka ya kamata yawa shuwagabannin tsaron Najeriya.