Bayan wallafa bidiyon Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode yana fada da matarsa inda tace masa ya daina cin zarafinta, Ministan yayi Martani.
Femi Fani Kayode yayi martanin ne bayan wallafa Bidiyon da Sahara Reporters ta yi inda ake zargin sa da ya ci zarafin matar tasa.
Saidai shi yace an fitar da Bidiyon ne kawai dan farfaganda. Yace bai ci zarafinta ba, ya kamata ne da wani mijin aure a gado kuma a lokacin da suke wannan cacar bakin wayar kawai ya kwace a hannunta amma bai ci zarafinta ba.
Yace ta rika duka da zagin ‘yan aikinsu da danginsa amma shi bai ci zarafinta ba.