fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Kamfanin BUA ya bi sahun Dangote shima zai gina matatar mai a jihar Akwa-Ibom

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin BUA ya shiga wata yarjejeniya da kamfanin Axens na kasar Faransa dan gina matatar man fetur.

 

Matatar man Fetur din za’a kammala ta ne nan da shekarar 2024 kuma zata rika samar da gangar mai 200,000 a kowace rana.

Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ne ya wakilci kamfanin nashi inda ya saka hannu a takardun yarjejeniyar a Faransa sai kuma shugaban kamfanin Axens, Jean Sentenac da shima ya saka hannu a madadin kamfanin nashi.

 

Za’a gina kamfanin ne a jihar Akwa-Ibom. Najeeiya dai na shigo da kashi 90 na man da take amfani dashi daga kasashen waje. Hutudole ya samo muku daga The Africa Report cewa bankuna da dama ne ke ta godon bada bashi dan ayi wannan aiki. Kuma Abdulsamad Rabiu ya bayyana cewa, aikin zai bada sakamakon da ake so lura da irin nasarorin da suka samu a baya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.