fbpx
Monday, May 23
Shadow

Kamfanonin sufurin jiragen sama za su dakatar da ayyukansu yayin da litar mai ta kai Naira 700 ga kowace lita

Kungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama na Najeriya (AON) ta sanar cewa mambobinta za su daina aiki daga ranar Litinin mai zuwa saboda tsadar da farashin man fetur, wanda ya kai Naira 700 ga kowace lita.

Masu kamfanonin sufurin jiragen saman sun sanar da haka ne cikin wata wasika da shugaban kungiyarsu Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya aika wa ministan sufurin sama Sanata Hadi Sirika.

Sakon da ke cikin wasikar ya sami amincewar dukkan shugabannin kamfanonin sufurin jiragen sama na kasar.

Ga wani abu cikin sakon nasu:

“Farashin man da muke amfani da shi na JetA1 ya tashi daga Naira 90 ga kowace lita guda zuwa Naira 700 a yanzu. babu kamfanin sufurin sama da zai iya daukan irin wannan tashin goron zabin a kankanin lokaci. Saboda haka ne muka rika tattaunawa da gwamnatin tarayya da majalisar tarayya da kamfanin mai na kasa NNPC da kuma dillalan man fetur da zummar sauko da farashin man kasa-kasa, matsalar da ta sa tikitin tafiyar da ba ta wuce sa’a guda ba ya kai naira 120,000.”

Karanta wannan  Hotunan ziyarar Amaechi a jihar Borno

A kan haka ne sanarwar ta ce: “kungiyar mu na sanar da jama’a cewa mambobinmu za su daina jigilar fasinja daga ranar Litinin 9 ga watan Mayu 2022 har illa ma sha Allahu.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.