Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kamin ya sauka daga mulki sai ya cika alkawuran da yawa ‘yan Najeriya a shekarar 2015.
Yace har yanzu yana nan kan bakarsa na kawo canji a kasarnan.
Shugaban ya bayyana bangaren samar da gidaje a matsayin wani bangare da gwamnatinsa ta yi kokari sosai akai.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wasu rukunin gidajen gwamnatin tarayya 68 data gina a akan titin Benin zuwa Auchi a jihar Edo.
Ya bayyana cewa a lokacin da yake neman mulki a 2015 ya yiwa ‘yan Najeriya alkawarin canji, to wadannan gidajen da aka gina suna daya daga cikin canje-canjen da ya kawo.