fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Kana neman daukaka? : Karanta yanda zaka sameta kamar yanda Ummi Zeezee tayi bayani

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa Ummi Zeezee tayi bayani, kamar yanda tace, a addinance akan yanda mutum zai samu daukaka daga gurin Allah, ga jawabin nata kamar haka:

“Salam, Ga kadan daga cikin “SIRRIN DAUKAKA ” da Abubuwan da ke kawo daukaka a musulunce sune:

1.Riko da littafin Allah.

2.Bin Sunnar Manzon Allah SAW.

3. Nisanta da zunubai.

4.barin Zalunci.

5.takaituwa akan halal.

6. Yawan ambaton Allah.

7.kiyaye Farillai.

8.yawaita adduoi gun ambaton Allah.

9.gujewa haram.

10.yawan yin sallolin nafila musamman da tsakiyar dare.

11.yawan yin salati ga annabi Muhammad s.a.w.

12.bin iyaye.

13.yin hakuri ga abunda kake neman daukaka akai.

14.barin wulakanta mutane.

15.yawan godiya ga Allah a duk halin daka tsinci kanka aciki.

Karanta wannan  Tura ta kai bango: kalli bidiyon yanda 'yan Inyamurai suka fara kama 'yan IPOB suna kashewa

Ammah mu sani Allah yana daukaka duk Wanda yaso ne a duniya kuma kafin a samu daukaka sai an dage da yin adduoi haka bayan an samu ma sai an cigaba da yin adduoi dan annabi Muhammad yace ko wace daukaka tana tare da hassada shiyasa ya zama dole a rika yin addua kafin a samu daukaka haka bayan an samu ma sai an cigaba da adduar in ba haka ba makiya suna iya dakushe Daukakar ta hanyar sirihi ko asiri ko tsafi ko baki.subhallah! Allah ka mana tsarI daga sharrin yan hassada amin.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.