fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Kano: Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa sakamakon garkuwa da kuma kashe yaro

Babbar Kotun Jiha mai lamba 5 da ke zamanta a Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Usman Na-Abba, ta yanke wa wani matashi, Ibrahim Ahmad Khalil hukuncin kisa sakamakon yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara 5 da haihuwa.

Tun da fari dai kotun ta ce ta samu Khalil da laifin garkuwa da yaron, mai suna Ahmad Ado, kuma ɗan ƴar uwarsa ne, ya kuma kashe shi.

Khalil dai ya ɗauke marigayi Ado a unguwar Karkasara da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a 2019, ya kuma nemi Naira miliyan 20 kuɗin fansa, daga baya kuma a ka daidaita da shi a kan Naira miliyan 2.

Sai dai kuma kafin a kai masa kuɗin fansar, sai Khalil ya kashe Ado ta hanyar bashi ƙwaya da kuma toshe masa baki da hanci da gam.

Karanta wannan  An saka dokar hana fitar dare a jihar Anambra

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Na-Abba ya zartar wa da wanda a ke ƙarar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun cikakun hujjoji da lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki ya ga batar a gabanta

Na-Abba ya ɗaure Khalil shekaru 14 a bisa laifin garukwa da mutune, sai kuma hukuncin kisa sakamakon laifin kisan kai.

Bayan kammala zaman kotun, lauyar wanda a kke ƙara, Barista Aisha Hassan Abdulkadir ta ce za su yi nazari akan hukuncin domin daukar mataki na gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.