Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakar Alarammomi 60 da zasu koyar a makarantun Allo daban-daban da aka zamantar a jihar.
Hakan ya fitone daga kwamishinan Ilimi na jihar, Malam Sanusi Kiru inda ya bayyanawa manema labarai a yau, Talata cewa malaman zasu fara aikine a makarantu 15 dake fadin kasar na Almajirai da aka zamanantar.
Yace gwamnan jihar yayi wannan kokari ne dan ganin ya kawai da tsarin da ake bi baya na makarantun Almajirci da babu tsari. Yace sabbin malaman zasu yi aiki ne Bunkure, Madobi da Bagwai.