Thursday, July 18
Shadow

Kano: Za mu bijirewa dokar ta-ɓaci – Kwankwaso ya zargi gwamnatin Najeriya da haddasa rashin tsaro

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Ahmed Bola Tinubu da yiwa jami’an tsaron Kano zagon kasa sakamakon kin cire jami’an da ke gadin hambararren Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado. Bayero.

Kwankwaso ya kuma zargi Gwamnatin Tarayya da yunkurin haifar da wani sabon salo na kungiyar ta’addanci da masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya.

Kwankwaso dai na mayar da martani ne kan halin da ake ciki a Kano inda ake zargin hukumomin tsaron gwamnatin tarayya na goyon bayan hambararren Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa, Madobi, Sanata Kwankwaso ya ce al’ummar Kano za su bijirewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga gwamnatin da aka kafa a jihar.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

“Muna da dimbin mabiya saboda mutane sun yi imani da mu, mu masu goyon bayan jama’a ne kuma gwamnatin NNPP ta kuduri aniyar yi musu hidima a duk inda suka zabe ta,” inji shi.

Kwankwaso ya kara da cewa, a matsayinmu na ‘yan siyasa, ba za mu nade hannayenmu muna kallon makiyan jihar suna lalata zaman lafiya a jiharmu ba, domin za mu yi duk mai yiwuwa wajen marawa gwamna baya don samun nasara. Ina farin ciki da cewa bai shagala ba kuma yana mai da hankali kan cimma burinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *