fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Kanu da Diouf sun jagoranci wasan tallafi ga ‘yan gudun hijira a Kano

Kanu
Tsoffin gwarzayen Afirka da suka kunshi Elhaji Diouf da Kanu Nwakwo da Garba Lawal da Tijjani Babangida sun kara da kungiyar Kano Pillars a wasan neman tara tallafin kudi ga ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.

‘Yan wasan sun amsa kira ne daga bangarori daban-daban na nahiyar Afirka, inda suka hada tawaga guda don yin wasa mai manufa daya. Duk da cewa shekaru sun fara kama galibinsu.
Tsoffin zaratan ‘Yan kwallon da suka yi fice a Afrika sun nuna wa duniya cewa har yanzu tauraruwarsu na haskawa.
Sai dai masu iya magana na cewa “Mai laya ya kiyayi mai zamani”, inda ‘yan wasan Kano Pillars, suka nuna tsoffin zakarun gasar Firimiyar Najeriya ne, ta hanyar nuna wa mazan-jiyan cewa lokacinsu ne.
Kano Pillars dai ta samu nasara a wasan da ci 2-1. Amma, rashin samun nasarar tsoffin ‘yan wasan na Afrika ba shi ne sakon da wasan ke son isarwa ba, illa manufar shirya wasan. Kuma ko ba komai dama ce ta sada zumunci tsakanin tsoffin ‘yan wasan da kuma takwarorinsu na yanzu.
Wasan dai ya ba daruruwan masoya kwallon kafa yin cudanya da tsoffin gwanayen wadanda tarihin kwallon kafa a Najeriya da ma Afrika ba zai taba mantawa da su ba musamman mafi yawancinsu suna cikin tawagar Najeriya da suka lashe zinari a wasannin Olympics a 1996.
Mutane sama da miliyan daya ne rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu. Kuma galibi tsoffin ‘yan wasa a duniya kan gudanar da wasa na musamman domin tara kudin tallafi ga wadanda wani bala’i ya shafa.
A Najeriyar dai an kfa gidauniya iri-iri, duka da nufin tallafa wa masu gudun-hijira, amma za a iya cewa wannan ne karon farko da gwarzayen kwallon kafa daga sassan nahiyar Afirka suka yi gangami don agazawa ta hanyar taka-leda, tare da nuna irin tasirin da kwallon kafa ke yi wajen hada kan duniya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Dalibai a kasar China na biyan Naira Dubu 43,000 a kowanne awa dan a koyar dasu yanda ake murmushi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *